Koma ka ga abin da ke ciki

HALITTARSA AKA YI?

Tururuwa Mai Wanka

Tururuwa Mai Wanka

 Kasancewa da tsabta yana da muhimmanci ga kowane kwaro idan yana so ya rika tashi ya rika hawan abubuwa da kuma sanin abubuwan da ke faruwa kewaye da shi. Alal misali, idan antenar tururuwa tana da datti hakan yana iya sa iyalinta su kasa sanin hanyar zuwa wurare, su kasa tattaunawa da kuma jin kamshi. Wani likitan dabobbi mai suna Alexander Hackmann ya ce, “A cikin iyalin tururuwa, ba za ka taba samu mai datti ba, domin ko a wane yanayi suke, suna neman hanyar tsabtace kansu.”

 Ka yi la’akari da wannan: Hackmann da abokan aikinsa sun yi bincike a kan yadda wasu irin tururuwa da ake kiran Camponotus rufifemur suke tsabtace antenarsu. Sun binciko cewa tururuwar takan share datti daga antenarta ta wajen lankwasa kafafunta kuma ta rika share antenar da kafafun. Wuraren kafafun da ke kama da bakin burushi mai karfi suna taimaka mata ta rika share manyan dattin da ke antenar. Kuma wuraren kafafun masu laushi suna cire kananan datti ta wajen yin amfani da gashin da ke kafafun tururuwar. Sa’annan wuraren kafafun da ke kama da burushi mafi kyau suna cire datti mafi kankanta.

 Ka kalli yadda tururuwar da ake kira Camponotus rufifemur take tsabtacce kanta

 Hackmann da abokan aikinsa sun gaskata cewa za a iya yin amfani da tsarin da kwari suke amfani da shi don tsabtacce kansu a masana’antu. Alal misali, ana iya bin wannan tsarin don a rika tsabtacce kananan abubuwa da ake sakawa a cikin na’urori sa’ad da ake kera su. Yin hakan zai taimaka don kada su dau datti da zai iya sa su ki yin aiki bayan an kera su.

 Mene ne ra’ayinka? Kana ganin cewa yadda tururuwar da ake kira Camponotus rufifemur ke tsabtacce kanta sakamakon juyin halitta ne? Ko akwai wanda ya halicce shi?