Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Zai Dace In Yi Abota da Mutane Dabam-dabam?

Zai Dace In Yi Abota da Mutane Dabam-dabam?

 Wani matashi mai suna Alan ya ce: “Ina son abokaina sosai, saboda haka, yana min wuya in yi abota da mutanen da ban san su ba.”

 Wata mai suna Sara ta ce: “Abokaina kadan ne kuma ba na so in dada wasu da ban saba da su ba.”

 Ra’ayinka daya ne da na Alan da Sara? Kana da abokai da kake jin dadin tarayya da su kuma ba ka son ka yi abota da wasu dabam?

 Idan haka ne, za ka koyi wani abu daga wannan talifin!

 Matsalar yin abokai da wasu irin mutane kawai

 Yin abokai da mutanen da ka fi sabawa da su ba laifi ba ne. Irin wadannan abokan za su iya sa ka kasance da gaba gadi, don ka san cewa sun amince da kai sosai.

 Wata ‘yar shekara 19 mai suna Karen ta ce: “Idan mutum yana da abokai da suke sonsa, zai so ya rika kasancewa tare da su kawai. Kuma idan mutum yana girma, zai so abokansa su amince da shi.”

 Ka sani? Yesu yana da abokai da yawa hade da manzanninsa 12, amma a cikin wadannan manzannin Bitrus da Yakub da kuma Yohanna ne suka fi kusa da shi.​—Markus 9:2; Luka 8:51.

 Amma, yin abokantaka da mutane iri daya kawai zai iya jawo wa mutum matsala. Alal misali:

  •   Zai iya hana ka samun abokan kirki.

     Wani dan shekara 21 mai suna Evan ya ce: “Idan tsararka ne kawai abokanka, hakan zai iya hana ka yin abokantaka da wasu da za ka iya koyan abubuwa masu kyau daga wurinsu.”

  •   Mutane za su iya ganin kamar kai mai girman kai ne.

     Wata ‘yar shekara 17 mai suna Sara ta ce: “Idan kana tarayya da mutane iri daya kawai, sauran mutane za su ga kamar ba ka son ka yi magana da su ne.”

  •   Zai iya sa ka zama mai cin zalin mutane.

     Wani dan shekara 17 mai suna James ya ce: “Mai yiwuwa kai ba ka cin zalin wasu, amma idan abokanka suna yin hakan, a hankali za ka soma dauka cewa yin hakan ba laifi ba ne ko ma ya zama maka abin dariya.”

  •   Zai iya jawo maka matsala, musamman ma idan kana so sai lalle-lalle ka yi abokantaka da wasu matasa.

     Wata ‘yar shekara 17 mai suna Martina ta ce: “Idan mutum daya a cikin abokanku bai da hankali, hakan zai iya shafan sauran wadanda kuke abokantaka da su.”

 Abin da za ka iya yi

  •   Ka bincika abin da ka fi darajawa.

     Ka tambayi kanka: ‘Ka’idodin wa nake bi a rayuwata? Abokaina suna taimaka mini in rika bin wadannan ka’idodin? Shin zan ci gaba da yin tarayya da su ko da hakan zai sa ni in yi abubuwa marar kyau?’

     Ka’idar Littafi Mai Tsarki: ‘Zama da miyagu takan bata halayen kirki.’​—1 Korintiyawa 15:33.

     Wata ‘yar shekara 14 mai suna Ellen ta ce: “Idan kana abokantaka da mutanen da ba sa bin ka’idodi iri daya da kai, hakan zai iya sa ka ka soma yin abubuwan da ba ka tsammani za ka yi ba.”

  •   Ka bincika abin da yake da muhimmanci a gare ka.

     Ka tambayi kanka: ‘Dangantakata da abokaina tana da karfi sosai da har za ta sa ni in yi abin da bai da kyau don kawai mu ci gaba da tarayyarmu? Me zan yi idan wani abokina ya yi abin da bai da kyau?’

     Ka’idar Littafi Mai Tsarki: ‘Wadanda nake kauna, ina tsauta musu.’​—Ru’ya ta Yohanna 3:19.

     Wata ‘yar shekara 22 mai suna Melanie ta ce: “Idan wani a cikin abokanka ya yi abin da bai da kyau, ba za ka so ka kai kararsa ba domin ba ka so wani abu ya faru da shi.”

  •   Ka kulla abota da mutane dabam-dabam.

     Ka tambayi kanka: ‘Zai dace in yi abokantaka da wadanda ban saba da su ba’?

     Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Ba dai kowa yana lura da nasa abu ba, amma kowane a cikinku yana lura da na wadansu.”​—Filibiyawa 2:4.

     Wani dan shekara 19 mai suna Brian ya ce: “Yawancin yaran da ba a san da su a makaranta ba suna fama ne da matsaloli a gida. Idan ka yi abokantaka da su, za ka ga cewa su ma suna da halaye masu kyau.”

 Gaskiyar al’amarin: Yin abokai da mutanen da ka fi sabawa da su ba laifi ba ne. Amma, za ka iya amfana idan ka kulla abota da wasu da ba ka saba da su ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka taimaki wadansu, su kuma za su taimake ka.”​—Misalai 11:​25, Littafi Mai Tsarki.