Koma ka ga abin da ke ciki

Mene Ne Littafi Mai Tsarki Ya Faɗa Game da Ista?

Mene Ne Littafi Mai Tsarki Ya Faɗa Game da Ista?

Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da

 Littafi Mai Tsarki bai ce a yi bikin Ista ba. Amma, idan ka bincika tarihi, za ka gano cewa Ista al’ada ce da aka ɗauko daga idodin ni’ima na dā. Ka yi la’akari da bayanan da ke gaba.

  1.   Suna: Littafin Encyclopædia Britannica ya ce: “Ba a san ainihin tushen sunan nan Ista ba; wani firist ɗan Anglo-Saxon mai suna Venerable Bede ya ɗauko sunan daga Eostre, allahiyar rani na Anglo-Saxon a ƙarni na 8.” Wasu kuma sun ce tushen daga Astarte ne, allahiyar ni’ima na ƙasar Finikiya da ake da irinta a Babila, wato, Ishtar.

  2.   Zomaye: Waɗannan alamu ne na ni’ima “da aka samo daga bukukuwan Turawa da na arnan Gabas ta Tsakiya da ake yi da rani.”​​—Encyclopædia Britannica.

  3.   Ƙwai: Littafin nan Funk & Wagnalls Standard Dictionary of Folklore, Mythology and Legend, ya ce: Neman ƙwan Ista da ake ganin zomayen Ista ne ke tanadarwa “ba wasan yara ba ne amma al’adar idin ni’ima ce.” Wasu sun gaskata cewa ƙwan Ista da ake sa musu launi “suna iya kawo farin ciki da ni’ima da lafiya da kuma kāriya a wata hanya mai al’ajabi.”​—Traditional Festivals.

  4.   Sababbin tufafi don Ista: “Ana ganin rashin hankali ne da kuma rashin sa’a a yi wa allahiyar Rani na Scandinavia, wato, Eastre, gaisuwa da tsofaffin tufafi.”​—The Giant Book of Superstitions.

  5.   Bukukuwa na fitowar rana: Waɗannan bukukuwan suna da alaƙa da bukukuwan da masu bauta wa rana a dā “suke yi a lokacin fitowar rana, sa’ad da suke marabtar rana tare da ikonsa na sa shuke-shuke su tsira.”​—Celebrations​—The Complete Book of American Holidays.

 Littafin nan The American Book of Days ya bayyana tushen Ista da cewa: “Babu shakka sa’ad da aka fara kafa Coci-coci an shigo da al’adun arna kuma aka mayar da su al’adun Kiristoci.”

 Littafi Mai Tsarki ya ce kada mu bi al’adun da ba su faranta wa Allah rai da da’awar cewa muna wa Allah ibada. (Markus 7:​6-8) Littafin 2 Korintiyawa 6:17 ya ce: “Ku ware [kanku], in ji Ubangiji, Kada ku taɓa kowane abu mara-tsarki.” Ista bikin arna ne kuma waɗanda suke son su faranta wa Jehobah bai dace su yi ba.