Koma ka ga abin da ke ciki

Su Waye Ne Mai Arzikin Nan da Liꞌazaru da Yesu Ya Ambata?

Su Waye Ne Mai Arzikin Nan da Liꞌazaru da Yesu Ya Ambata?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Mai arziki da Liꞌazaru suna cikin wani labari ne da Yesu ya bayar. (Luka 16:​19-31) A labarin, mutanen nan suna kwatancin mutane kashi biyu ne: (1) shugabannin addinin Yahudawa a zamanin Yesu masu fahariya kuma na (2) talakawa masu zuciyar kirki da suka saurari sakon Yesu.

A talifin nan za mu tattauna

 Abin da Yesu ya fada game da mai arzikin nan da Liꞌazaru

 A littafin Luka sura 16, Yesu ya ba da labarin mutane biyu da rayuwarsu ta canja gabaki daya.

 Ga labarin nan da Yesu ya bayar a takaice: Wani mutum mai arziki yana jin dadin rayuwarsa. Saꞌan nan akwai wani maroki da yake zama a bakin kofarsa mai suna Liꞌazaru. Yana alla-alla a ba shi ko da sauran abincin da ya fadi daga teburin mai arzikin nan. Ana nan sai Liꞌazaru ya mutu kuma malaꞌiku suka kai shi ya zauna a gefen Ibrahim. Mai arzikin nan ya mutu kuma aka bizine shi. A labarin, an nuna cewa bayan da suka mutu, sun ci gaba da rayuwa. An sa mai arzikin a wuta yana konewa, sai ya roki Ibrahim ya gaya ma Liꞌazaru ya sa yatsansa a ruwa ya diga masa harshe don ya sami sanyi. Ibrahim bai yarda ya yi abin da mai arzikin ya roka ba domin ya ce su biyun yanayinsu yanzu ya canja. Kuma ya ce yanzu akwai wani rami mai zurfi a tsakaninsu da ba za a iya haye wa ba.

 Shin labarin nan ya faru da gaske ne?

 Aꞌa. Labarin nan kwatanci ne da Yesu ya bayar don ya koya mana wani darasi. Masana ma sun ce wannan labari ne kawai. Alal misali, akwai wani kan magana a juyin Littafi Mai Tsarki na Luther na 1912 da ya ce wannan labari ne kawai. Ban da haka, wani karin bayani na Jerusalem Bible na Katolika, ya ce “wannan labari ne kawai da ba ya nuni ga wani abu da ya taba faruwa.”

 Shin darasin da Yesu yake koyarwa shi ne mutane sukan rayu bayan sun mutu? Ko kuma yana nufin cewa za a kone wasu mutane da wuta bayan sun mutu? Ko kuma Ibrahim da Liꞌazaru suna sama ne? Akwai wasu bayanai da yawa da suka nuna cewa ba haka ba ne.

 Alal misali:

  •   Da a ce mai arzikin yana cikin wuta na zahiri ne, da zafin wutar ba zai busar da digon ruwan da ke yatsar Liꞌazaru ba?

  •   Ko da a ce ruwan bai bushe ba, da digon ruwan zai iya sa mai arzikin nan ya dan ji sanyi daga zafin wutar?

  •   Ya za a ce Ibrahim yana sama da yake a lokacin da Yesu ya ba da wannan labarin, ya ce babu wanda ya taba zuwa sama?​—Yohanna 3:13.

 Shin labarin nan yana goyon bayan koyarwar nan cewa za a kona mutane da wuta?

 Aꞌa. Ko da yake wannan labarin bai faru da gaske ba. Duk da haka, wasu suna ganin cewa wannan labarin yana goyon bayan koyarwar nan cewa masu adalci za su je sama, mugaye kuma za a kone su da wuta. a

 Raꞌayinsu daidai ne? Aꞌa.

 Koyarwar wutar jahannama bai jitu da abin da Littafi Mai Tsarki ya fada game da yanayin matattu ba. Alal misali, bai ce dukan mutane masu adalci da suka mutu za su je sama suna jin dadi saꞌan nan a rika kona mugaye a wutar jahannama ba. A maimakon haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Masu rai sun sani za su mutu, amma matattu ba su san kome ba. Ba su da sauran lada, ba a sake tunawa da su.”​—Mai-Waꞌazi 9:5.

 Mene ne maꞌanar kwatancin mai arziki da Liꞌazaru?

 Labarin ya nuna cewa akwai mutane kashi biyu da yanayin su yana gab da canjawa.

 Mai arzikin nan yana wakiltar malaman addinin yahudawa, “masu son kudi.” (Luka 16:14) Ko da yake sun saurari abin da Yesu ya fada, sun yi adawa da shi. Wadannan malaman addini suna rena talakawa.​—Yohanna 7:49.

 Liꞌazaru yana wakiltar talakawan da suka karbi sakon Yesu da malaman addinan suka rena.

 Yanayin mutane kashi biyun nan ya canja farat daya.

  •   Malaman addinan nan sun dauka cewa suna da amincewar Allah. Amma da yake sun ki karban sakon Yesu, Allah ya ki su da sujadar su. A gaban sa sun zama kamar matattu. Sakon nan da Yesu da mabiyansu suka yi waꞌazinsa ya sa su fushi, kamar kona su yake yi.​—Matiyu 23:​29, 30; Ayyukan Manzanni 5:​29-33.

  •   Yanzu talakawan nan da malaman addinai suka yi banza da su suna jin dadi. Yawancin su sun karbi sakon Littafi Mai Tsarki da Yesu ya koyar kuma sun amfana sosai. Yanzu suna da damar more alherin Allah har abada.​—Yohanna 17:3.

a Wasu juyin Littafi Mai Tsarki sun yi amfani da kalmar nan “jahannama” don su kwatanta inda mai arzikin nan ya je bayan da ya mutu. Amma ainihin kalmar Hellenanci (Hades) da aka yi amfani da ita a Luka 16:23 tana nufin kabari.