Koma ka ga abin da ke ciki

Mene Ne Zan Iya Yin Addu’a a Kai?

Mene Ne Zan Iya Yin Addu’a a Kai?

Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da

 Za ka iya addu’a game da duk abin da ya jitu da nufin Allah kamar yadda aka bayyana a Littafi Mai Tsarki. “Idan mun roki komi daidai da nufinsa, [wato Allah], yana jinmu.” (1 Yohanna 5:14) Za ka iya ambata abubuwan da suke damunka? E. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku zazzage zuciyarku a gaban [Allah].”—Zabura 62:8.

Misalan abubuwan da za ka iya yin addu’a a kansu

  •   Bangaskiya ga Allah.—Luka 17:5.

  •   Ruhu mai tsarki ko ikon Allah don ya taimake ka yin abin da ya dace.—Luka 11:13.

  •   Karfi don ka jimre da matsaloli kuma ka guji jaraba.—Filibiyawa 4:13.

  •   Kwanciyar rai ko kuma natsuwa.—Filibiyawa 4:6, 7.

  •   Hikima don tsai da shawarwari masu kyau.—Yakub 1:5.

  •   Taimako don bukatu na yau da kullum.—Matta 6:11.

  •   Neman gafarar zunubai.—Matta 6:12.