Koma ka ga abin da ke ciki

Akwai “Zunubai Bakwai da Ke Sa Mutuwa”?

Akwai “Zunubai Bakwai da Ke Sa Mutuwa”?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Littafi Mai Tsarki bai kwatanta jerin “zunubai bakwai da ke sa mutuwa” ba. Amma ya koyar cewa yin zunubai masu tsanani zai hana mutum samun ceto. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce “ayyukan jiki” kamar yin lalata da bautar gunki da sihiri da yawan fushi da kuma yin maye suna cikin zunubai masu tsanani. Ya kuma ce: “Wadanda ke aika wadannan al’amura ba za su gaji mulkin Allah ba.”—Galatiyawa 5:19-21. a

Amma Littafi Mai Tsarki ya ambata abubuwa bakwai da Ubangiji yake kyamarsu, ko ba haka ba?

 Kwarai kuwa. Littafin Misalai 6:16 ya ce: “Akwai abu shida wadanda Ubangiji ya ki: I, har bakwai ma wadanda ransa yake kyamarsu.” Amma, ba a ambata dukan zunubai a cikin littafin Misalai 6:17-19 ba. Maimakon haka, an kwatanta ainihin ayyukan da ba su kyau da suka hada da tunaninmu da furucinmu da abubuwan da muke yi. b

Mene ne “zunubi da ke na mutuwa”?

 Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa dukan zunubai suna kai ga mutuwa. (1 Yohanna 5:16) Amma za a cece mu daga zunubi da mutuwa ta wurin hadayar fansa da Yesu Kristi ya ba da. (Romawa 5:12; 6:23) Saboda haka, fansa da Kristi ya ba da ba ta ceton mutum daga “zunubi da ke na mutuwa.” Mutumin da yake yin irin wannan zunubin ya yi niyyar bin tafarki na zunubi kuma ba zai taba canja halinsa ba. Don haka, Littafi Mai Tsarki ya kuma ce “ba za a gafarta” wa mutum irin wannan zunubin ba.—Matta 12:31; Luka 12:10.

a Ko da yake an lissafa zunubai masu tsanani guda 15 a littafin Galatiyawa 5:19-21, hakan ba ya nufin cewa sun kāre ke nan, don bayan ya lissafa su, Littafi Mai Tsarki ya ce “da irin wadannan.” Saboda haka, an karfafa mai karatu ya yi amfani da basira don ya fahimci abubuwan da ba a ambata a ciki ba amma suna cikin ‘irin wadannan’ zunuban.

b Littafin Misalai 6:16 yana dauke da misalin karin magana na Ibrananci da ya nuna bambanci da ke tsakanin furuci na farko da na biyun. Ana yawan ganin irin wannan furucin a cikin Nassosi.—Ayuba 5:19; Misalai 30:15, 18, 21.