Koma ka ga abin da ke ciki

GANAWA | ANTONIO DELLA GATTA

Dalilin da Ya Sa Wani Fada Ya Bar Cocinsa

Dalilin da Ya Sa Wani Fada Ya Bar Cocinsa

BAYAN Antonio Della Gatta ya yi shekara tara yana makaranta a kasar Roma, sai aka nada shi fada a shekara ta 1969. Daga baya, ya zama shugaban wata makarantar fada kusa da birnin Naples a kasar Italiya. A lokacin da yake wurin, ya yi bincike da tunani sosai kuma ya ga cewa Cocin Katolika, ba ya koyar da abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Ya yi magana da mawallafan Awake! game da famar da ya yi.

Don Allah ka dan ba mu tarihinka.

An haife ni a kasar Italiya a 1943. Na yi girma tare da ’yan’uwana maza da mata a wani kauye kuma mahaifinmu manomi ne da kuma kafinta. An yi renonmu a Cocin Katolika.

Me ya sa ka so ka zama fada?

Tun ina karami nake jin dadin koyarwar fada a coci. Idan na ga yadda suke magana da irin hidimomin da suke yi a coci, abin yana burge ni. Da nake shekara 13, mahaifiyata ta kai ni makarantar da ake koyar da yara don su zama fada.

Shin kun yi nazarin Littafi Mai Tsarki a makarantar?

A’a. Da na kai shekara 15, wani malamina ya ba ni kofin Linjila da ke dauke da tarihin Yesu da hidimarsa, kuma na karanta littafin sau da yawa. Da nake shekara 18 kuma, na je Roma don in yi karatu a jami’o’in da ke karkashin Paparoma. Na karanta tarihi da ilimin falsafa da halin mutane da ilimin sanin Allah kuma na yi nazarin yaren Latin da Girkanci. Ko da yake mukan haddace nassosin Littafi Mai Tsarki kuma akan karanta mana shi a coci a ranar Lahadi, amma ba ma nazarinsa.

Da yake ka zama shugaban makaranta, hakan ya kunshi koyarwa ne?

Yawancin aikina ya kunshi kula da harkokin makarantar. Amma na koyar da dalibai a kan Majalisa na Biyu na Vatican na Cocin Katolika.

Me ya sa ka fara shakkar cocinku?

Abubuwa uku ne suka fi damuna. Cocin yana shiga harkokin siyasa. Shugabannin cocin da kuma membobinsu suna halayya marasa kyau kuma ba a musu kome. Ban da haka, ban amince da wasu abubuwan da ake koyarwa a cocin ba. Alal misali, ta yaya za a ce Allah mai kauna zai hukunta mutane har abada bayan sun mutu? Ban da haka, shin Allah yana so mu rika amfani da carbi sa’ad da muke masa addu’a kuma mu rika maimaita addu’ar sau da yawa? *

Me ka yi?

Na yi addu’a sosai ga Allah ina zub da hawaye cewa ya taimaka mini. Ban da haka ma, na sayi juyin Jerusalem Bible na Cocin Katolika da aka fassara zuwa yaren Italiya kuma na soma karanta shi. Wata rana, a ranar Lahadi da na dawo daga coci kuma ina cire kaya, sai wasu mutane biyu suka shigo. Sun ce min su Shaidun Jehobah ne. Mun yi fiye da awa daya muna tattaunawa game da Littafi Mai Tsarki da kuma yadda za a gane addini na gaske.

Mene ne ra’ayinka game da Shaidun Jehobah da suka zo?

Yadda suke bayyana Littafi Mai Tsarki da tabbaci da kuma yadda suka yi amfani da juyin littafina na Katolika, ya burge ni sosai. Bayan haka, sai wani Mashaidi mai suna Mario ya fara kawo min ziyara. Shi mai hakuri ne kuma ba ya fasa zuwa. Yana zuwa kowace ranar Asabar da safe daidai karfe tara ko da yaya yanayin wuri yake.

Yaya wasu fada suka ji game da ziyarar da Shaidun Jehobah suke maka?

Na ce musu su zo mu rika nazari tare, amma ba su dauki hakan da muhimmanci ba. Ni dai na ji dadin nazarin. Na koyi abubuwa kamar abin da ya sa Allah ya kyale mugunta da shan wahala, dā ma wannan batun ya dade yana damu na.

Shin wadanda suke gaba da kai sun yi kokarin hana ka nazarin ne?

A shekara ta 1975, na je kasar Roma sau da yawa don in bayyana musu ra’ayina. Wadanda suke gaba da ni sun yi kokarin canja ra’ayina, amma ba wanda ya yi amfani da Littafi Mai Tsarki. A karshe a ranar 9 ga Janairu na shekara ta 1976, na rubuta wasika kuma na gaya musu cewa ni ba dan Katolika ba ne kuma. Bayan kwana biyu, na bar makarantar kuma na shiga jirgi domin na halarci taron Shaidun Jehobah a lokaci na farko. Da na je, sai na ga cewa babban taro ne da ya kunshi ikilisiyoyi da yawa. Abubuwan da suke yi ya sha bambam da wadanda muke yi a cocinmu! Kowannensu a wurin yana da Littafi Mai Tsarki kuma yana bi sa’ad da aka ce a karanta. An tattauna batutuwa da yawa a taron.

Me iyalinka suka yi game da hakan?

Yawancinsu sun tsananta mini sosai. Amma na gano cewa akwai wani dan’uwana da yake nazari da Shaidun Jehobah kuma yana zama a yankin Lombardy da ke arewacin Italiya. Na je wurinsa kuma Shaidun da suke wurin sun nema min aiki da gida. A shekarar ne na yi baftisma a matsayin Mashaidin Jehobah.

Daga baya, na kusaci Allah

Kana da-na-sani?

Ko kadan! Daga baya, na kusaci Allah domin na koyi gaskiya game da shi daga Littafi Mai Tsarki, ba daga ilimin falsafa ko al’adun coci ba. Kuma zan iya koyar da mutane da tabbaci.

^ sakin layi na 13 Littafi Mai Tsarki ya ba da amsar tambayoyin nan da kuma wasu tambayoyi da dama. Ka duba karkashin KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI > AMSOSHIN TAMBAYOYIN LITTAFI MAI TSARKI.