Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

2 Zai Sa Ka Magance Matsaloli

2 Zai Sa Ka Magance Matsaloli

Wasu matsaloli na rayuwa suna iya damun mu har na tsawon lokaci. Wataƙila suna farawa a hankali-hankali ba tare da saninmu ba. Shin Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu iya magance matsalolin da muka daɗe muna fuskanta? Ga wasu misalai.

YAWAN DAMUWA

Rosie ta ce, “Ina yawan damuwa a kan wasu abubuwan da ba su da muni kamar yadda nake zatonsu.” Waɗanne ayoyin Littafi Mai Tsarki ne suka taimaka mata? Ɗaya daga cikinsu shi ne Matta 6:​34, wurin ya ce: “Kada fa ku yi alhini a kan gobe: gama gobe za ta yi alhini don kansa. Wahalar yini ta ishe shi.” Yanzu Rosie ta ce abin da Yesu ya faɗa ya taimaka mata ta daina damuwa a kan abin da zai faru gobe. Ta kuma ce, “Ina da matsaloli irin na yau da kullum, amma ba na ƙara wa kaina wasu matsaloli ta wurin damuwa da abin da wataƙila zai faru gobe ko kuma ba zai ma faru ba.”

Yasmine ma ta lura cewa matsalolinta suna so su fi ƙarfinta. Ta ce: “Nakan yi kuka na ’yan kwanaki a kowane mako kuma a wasu lokuta ba na iya yin barci. Na gano cewa yawan damuwa zai cinye ni ɗanye.” Wace aya ce ta taimaka mata? Ta ce 1 Bitrus 5:7 ce. Ayar ta ce: “Kuna zuba dukan alhininku a bisansa, domin yana kula da ku.” Yasmine ta ce: “Da shigewar lokaci, na ci gaba da yin addu’a ga Jehobah kuma ya amsa addu’ata. Na ji kamar an sauke min kaya mai nauyi daga kaina. Nakan damu a wasu lokuta, amma yanzu na san yadda zan bi da su.”

RASHIN NATSUWA

Wata mata mai suna Isabella ta ce: “Ina ganin rashin natsuwa abu ne da ake iya gādan sa, domin mahaifina yana da irin halin. Nakan ƙyale muhimman abubuwa da ya kamata in yi kuma in zauna kawai ko na riƙa kallon talabijin. Halin ba shi da kyau domin yana ƙara gajiya kuma ba zai sa ka natsu ka yi aiki mai kyau ba.” Ƙa’idar da ke cikin littafin 2 Timotawus 2:15 ce ta taimaka mata. Ayar ta ce: “Ka yi ƙoƙari ka miƙa kanka yardaje ga Allah, ma’aikaci wanda babu dalilin kunya gare shi.” Isabella ta ce, “Ba na son Jehobah ya yi baƙin ciki domin rashin natsuwata.” Yanzu ta kyautata halinta.

Kelsey ma ta ce: “Nakan bar aikin da ya kamata in yi sai lokaci ya kure kafin na fara yi. Hakan yana sa ni kuka da baƙin ciki kuma in gagara yin barci. Ba na jin daɗin hakan.” Littafin Misalai 13:16 ya taimaka wa Kelsey, wurin ya ce: “Kowane mutum mai-hankali yakan yi aikinsa bisa ga ilimi: Amma wawa yakan bayana wauta.” Ta bayyana abin da ta koya bayan ta yi bimbini a kan ayar, ta ce: “Yana da kyau mutum ya ɗau mataki kuma ya tsara aikin da zai yi tun da wuri. A yanzu ina tsara ayyukan da zan yi tun da wuri kuma ina ajiye takardar a kan teburina. Yin hakan ya sa ba na barin aikina har sai lokaci ya kure.”

KAƊAICI

Kirsten ta ce: “Maigidana ya bar ni da yara guda huɗu.” Wace ƙa’idar Littafi Mai Tsarki ce ta taimaka mata? Littafin Misalai 17:17 ya ce: “Aboki kullayaumi ƙauna yake yi, kuma an haifi ɗan’uwa domin kwanakin shan wuya.” Kirsten ta nemi taimakon ’yan’uwa a ikilisiya. Wane taimako ta samu? Ta ce: “Abokaina sun kasance tare da ni a hanyoyi da dama! Wasu sun ajiye min abinci da furanni a ƙofar gidana. Sau uku ’yan’uwa sun taimaka mini sa’ad da nake ƙaura. Wani kuma ya nema min aiki. A kullum abokaina suna a shirye su taimaka mini.”

Delphine da muka ambata ɗazun ma ta yi fama da kaɗaici. Ga abin da ta faɗa bayan rashin da ta yi: “Na ji na yi dabam da sauran mutane domin kowa yana da na kusa da shi, amma ni ba ni da kowa.” Littafin Zabura 68:6 yana ɗaya daga cikin nassosin da suka taimaka mata. Wurin ya ce: “Allah yana maida masu-kaɗaici su zauna cikin iyalai.” Ta ce: “Na san cewa ayar ba ta nufin gida na zahiri kawai ba. Maimakon haka, na fahimci cewa Allah ya tanadar mana da ’yan’uwa a ikilisiya kuma a wurin ne muke samun kāriya da ta’aziya da kuma ƙauna daga masu ƙaunar Jehobah. Amma na san cewa kafin in iya kusantar wasu, sai na fara kusantar Jehobah. Kuma littafin Zabura 37:4 ya taimaka min in yi hakan. Ayar ta ce: ‘Ka faranta zuciyarka cikin Ubangiji kuma za ya kuwa biya maka muradin zuciyarka.’”

A ƙarshe, Delphine ta ce: “Na gane cewa ina bukatar in manne wa Jehobah sosai, domin shi ne abokin kirki da babu kamar sa. Sai na tsara ayyuka da zan riƙa yi da wasu ’yan’uwa don in sami damar yin abota da waɗanda suke ƙaunar Jehobah. Na koya yadda zan mai da hankali a kan halayen kirki na wasu ba kurakuransu ba.”

Ko abokai waɗanda suke bauta wa Jehobah ma ajizai ne. Shaidun Jehobah ma suna fama da wasu matsaloli kamar yadda kowa ma yake yi. Amma Littafi Mai Tsarki yana koyar da mutane su riƙa taimaka ma waɗanda suke fama da matsaloli. Shi ya sa yana da kyau ka yi abokantaka da mutanen da suke bauta wa Allah. Amma ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki za su iya magance matsaloli da ’yan Adam ba su iya magance su a yau ba, kamar cututtuka masu tsanani da kuma mutuwa?

Bin shawarar Littafi Mai Tsarki zai taimaka maka ka sami abokan kirki