HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Janairu 2017

Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari na 27 ga Fabrairu zuwa 2 ga Afrilu, 2017.

Sun Ba da Kansu da Yardar Rai

Da farko ‘yan’uwa mata marasa aure da yawa da suka yi hidima a wata kasa sun yi jinkiri kaura zuwa kasashen. Mene ne ya taimaka musu su kasance da karfin zuciya? Mene ne suka koya a hidimarsu a wata kasa?

Ka Dogara ga Jehobah Kuma Ka Yi Alheri

Jehobah yana farin cikin yi mana abin da ba za mu iya yi da kanmu ba. Amma yana so mu yi abin da za mu iya yi. Ta yaya jigonmu na shekara ta 2017 ya sa muka kasance da ra’ayin da ya dace?

Ka Yi Amfani da ‘Yancinka a Hanyar da Ta Dace

Mene ne ‘yanci kuma me Littafi Mai Tsarki ya koyar game da shi? Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja ‘yancin wasu?

Shin Kasancewa da Tawali’u Tsohon Yayi Ne?

Mene ne tawali’u, kuma wace alaka ce yake tsakanin tawali’u da saukin kai? Me ya sa yake da muhimmanci mu kasance da wannan halin?

Za Ka Iya Zama Mai Tawali’u Sa’ad da Kake Fuskantar Jaraba

Ta yaya za mu iya kasancewa da tawali’u sa’ad da yanayinmu ya canja, sa’ad da ake yi mana ba’a, sa’ad da ake yabonmu, da kuma sa’ad da muke son mu yanke shawarwari?

“Ka Danka ma Mutane Masu-Aminci”

Ta yaya tsofaffi za su taimaka wa matasa su dauki karin aiki a hidimarsu? Ta yaya matasa za su nuna cewa suna daraja ‘yan’uwan da suka dade sun yin ja-goranci?

Ka Sani?

Ta yaya ake daukan wuta daga waje zuwa waje a zamanin dā?