Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Me Ya Sa Allah Ba Ya Amsa Dukan Addu’o’i?

Me Ya Sa Allah Ba Ya Amsa Dukan Addu’o’i?

Ubanmu na sama, wato Jehobah, yana jin daɗin sauraron addu’o’in da muke yi daga zuciyarmu. Amma akwai abubuwan da idan muka yi, za su sa Allah ba zai ji addu’armu ba. Waɗanne abubuwa ke nan? Me ya kamata mu riƙa tunawa a duk lokacin da muke addu’a? Ga abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa.

“In kuwa kuna addu’a, kada ku yi ta maimaitawar banza.”​—Matiyu 6:​7, Littafi Mai Tsarki.

Jehobah ba ya so mu riƙa maimaita addu’o’in da muka haddace ko mu karanta su daga wani littafi. A maimakon haka, yana so mu gaya masa abin da ke zuciyarmu. Ya za ka ji idan abokinka ya zo ya yi ta maimaita maka abu ɗaya kowace rana? Abokan kirki suna gaya wa juna abin da ke zuciyarsu. Idan muna gaya wa Ubanmu na sama abin da ke zuciyarmu, hakan zai nuna cewa muna ɗaukansa a matsayin abokinmu.

“Sa’ad da kukan roƙa ba ku samu ba, gama kukan roƙa da mugun nufi.”​—Yaƙub 4:3.

Bai kamata mu ɗauka cewa Allah zai amsa addu’ar da muke yi game da wani abin da ba zai so mu yi ko mu samu ba. Alal misali, idan mutum ya je yin caca kuma ya roƙi Allah ya ba shi sa’a, kana ganin Allah zai amsa addu’ar? Allah da kansa ya ce kada mu zama masu haɗama kuma kada mu yi imani da sa’a da ƙaddara. (Ishaya 65:11; Luka 12:15) Don haka, Jehobah ba zai taɓa amsa irin wannan addu’ar ba. Kafin Allah ya amsa addu’armu, Kalmar Allah ta gaya mana cewa dole ne addu’ar ta jitu da nufinsa.

“Idan mutum ya ƙi kasa kunne ga doka, addu’arsa ma abin ƙyama ce.”​—Karin Magana 28:9.

A zamanin Isra’ilawa, Allah ya ƙi ya amsa addu’o’in waɗanda suka yi masa rashin biyayya. (Ishaya 1:​15, 16) Allah bai canja ba har wa yau. (Malakai 3:6) Idan muna so Allah ya amsa addu’o’inmu, dole ne mu yi iya ƙoƙarinmu mu bi dokokinsa. Amma, idan mun yi abubuwan da ba su dace ba a dā fa? Hakan yana nufin Allah ba zai saurare mu ba? Ko kaɗan. Allah yana ƙaunarmu, don haka, zai gafarta mana idan muka tuba kuma muka yi iya ƙoƙarinmu mu faranta masa rai.​—Ayyukan Manzanni 3:19.