Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yadda Za A Taimaka Wa Masu Fama da Matsalar Kwakwalwa

Yadda Za A Taimaka Wa Masu Fama da Matsalar Kwakwalwa

LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “A koyaushe aboki yana nuna ƙauna, an haifi ɗanꞌuwa kuwa domin taimako a kwanakin masifa.”​—KARIN MAGANA 17:17.

Abin da Hakan Yake Nufi

Idan wani abokinmu yana fama da matsalar ƙwaƙwalwa, za mu iya ji kamar ba abin da za mu iya yi. Amma za mu iya nuna cewa mun damu da shi ta wurin taimaka masa ya jimre da matsalar da yake fama da ita. Ta yaya za mu yi hakan?

Yadda Yin Hakan Zai Taimaka

Ka “kasance mai saurin ji.”​—YAKUB 1:19.

Wani abu mafi kyau da za mu iya yi wa abokinmu shi ne mu saurare shi saꞌad da yake magana. Kada ka ji kamar dole ne ka amsa masa duk abin da ya faɗa. Ka tabbatar masa cewa kana sauraronsa kuma ka nuna ka damu da shi. Ka yi ƙoƙari ka fahimci yadda yake ji kuma kada ka kushe shi. Ka tuna cewa zai iya faɗin abubuwan da bai kamata ba, kuma ya yi da-na-sani daga baya.​—Ayuba 6:​2, 3.

“Ku ƙarfafa waɗanda ba su da ƙarfin zuciya.”​—1 TASALONIKAWA 5:14.

Wataƙila abokinka yana damuwa sosai, ko kuma yana ji kamar ba shi da amfani. Idan ka nuna ka damu da shi, hakan zai ƙarfafa shi, ko da ba ka san abin da za ka faɗa ba.

“A koyaushe aboki yana nuna ƙauna.”​—KARIN MAGANA 17:17.

Ka yi iya ƙoƙarinka ka taimaka masa. Maimakon ka ɗauka cewa ka san yadda za ka taimaka masa, ka tambaye shi abin da yake so ka yi masa. Idan abokinka ya rasa yadda zai bayyana abin da yake bukata, ka tambaye shi ko za ku iya yin wasu abubuwa tare, kamar fita yawo. Ko ka tambaye shi ko za ka iya masa cefane, ko shara ko kuma wasu ayyuka na yau da kullum.​—Galatiyawa 6:2.

Ku kasance da “haƙuri.”​—1 TASALONIKAWA 5:14.

Ba kowane lokaci ne abokinka zai so ya yi magana ba. Ka gaya wa abokinka cewa kana shirye ka saurare shi a kowane lokaci idan yana so ya yi magana. Rashin lafiyar abokinka zai iya sa ya yi ko kuma ya faɗi wani abin da zai ɓata maka rai. Zai iya fasa zuwa ko yin abin da kuka shirya za ku yi ko kuma ya ɓata rai. Ka yi ƙoƙari ka fahimci yanayinsa kuma ka kasance da haƙuri yayin da kake taimaka masa.​—Karin Magana 18:24.

Yana da Muhimmanci Ka Taimaka Wa Abokinka

Wata mai suna Farrah, a da ƙawarta take fama da matsalar cin abinci da tsananin damuwa da kuma ciwon baƙin ciki mai tsanani ta ce: “Na yi ƙoƙari in tabbatar mata cewa za ta iya yi mini magana a kowane lokaci. Ko da yake ban san yadda zan magance matsalolinta ba, na yi iya ƙoƙari in saurare ta. A wasu lokuta abin da yake kwantar mata da hankali shi ne, wani ya saurare ta.”

Wata mai suna Ha-eun da take fama da ciwon baƙin ciki mai tsanani ta ce: “Ɗaya daga cikin ƙawayena tana da hankali kuma tana ƙarfafa ni. Ta gayyace ni in zo gidanta don mu ci abinci mai daɗi. Ta nuna tana ƙaunata sosai kuma hakan ya min sauƙi in bayyana mata abin da ke damuna. Abin da ta yi ya ƙarfafa ni sosai!”

Wani mai suna Jacob da matarsa take fama da baƙin ciki mai tsanani ya ce: “Haƙuri yana da muhimmanci sosai. Idan matata ta yi min wani abin da ya ɓata min rai, nakan tuna cewa rashin lafiyarta ne yake sa ta yi hakan. Hakan yana taimaka min in guji yin fushi kuma in ci gaba da yin haƙuri da ita.”

Wani mai suna Enrico da ke fama da cutar tsananin damuwa ya ce: “Matata ce take taimaka mini kuma take ƙarfafa ni. Idan damuwa ya yi min yawa, ba ta tilasta min in yi abin da ba na so in yi. A wasu lokuta, hakan yakan sa ba ta yin wasu abubuwan da take so ta yi. Tana da muhimmanci a gare ni don tana da kirki kuma ba ta nuna son kai.”

a An canja sunayen.