Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

“Idanunka sun ga gaɓoɓin jikina kafin su cika.”​—ZABURA 139:16.

Allah Yana Fahimtar Yanayinka Kuwa?

Allah Yana Fahimtar Yanayinka Kuwa?

ABIN DA HALITTU SUKA KOYA MANA

Ka ɗan dakata ka yi tunani a kan irin dangantakar da ke tsakanin tagwaye. Tagwaye suna kasancewa da dangantaka ta kud da kud da juna sosai. Wata mata wadda ita ma ’yar biyu ce da kuma direktan Cibiyar da Ke Nazari a Kan ’Yan biyu mai suna Nancy Segal ta ce, wasu ’yan biyu “suna iya magana kuma su fahimci juna sosai.” Wata mata da ita ma ’yar biyu ce ta ce: “Mun san kome game da junanmu.”

Me ya sa ’yan biyu suke da irin wannan dangantakar? Bincike ya nuna cewa yadda iyaye suke renon yaran da kuma inda yaran suka taso ne suke sa su kasance da wannan dangantakar. Amma mafi muhimmanci shi ne, ’yan biyu suna da kwayoyin hali iri ɗaya.

KA YI LA’AKARI DA WANNAN: Hakika, Mahaliccinmu ya fi kowa sanin yanayinmu. Shi ya sa Dawuda ya ce: “Kai ne ka halicci kayan cikina, ka harhaɗa ni a cikin mamata. Ƙasusuwan jikina ba a ɓoye suke a gare ka ba, sa’ad da aka harhaɗa ni a asirce, . . . A cikin littafinka an rubuta yawan kwanakin da aka shirya domina.” (Zabura 139:​13, 15, 16) Allah ne kaɗai ya san yadda kwayoyin halinmu suke aiki da kuma abubuwan da muke fuskata a rayuwa da suke sa mu canja halinmu. Tun da Allah ya san yanayinmu da kuma kwayoyin hali da ke jikinmu, hakan ya tabbatar mana cewa yana fahimtar yanayinmu sosai.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE GAME DA HIKIMAR ALLAH

Dawuda ya yi addu’a ya ce: “Ya Yahweh, ka riga ka bincike ni ka kuwa san ni. Kai kakan san zamana da tashina, kakan gane da tunanina tun daga nesa. Kafin ma kalma ta fita daga bakina, ya Yahweh, ka riga ka sani kakaf.” (Zabura 139:​1, 2, 4) Ƙari ga haka, Jehobah ya san yadda muke ji a zuciyarmu kuma yana da ikon sanin “niyyar kowace zuciya.” (1 Tarihi 28:9; 1 Sama’ila 16:​6, 7) Mene ne ayoyin nan suka koya maka game da Allah?

Ko da yake ba za mu iya gaya wa Mahaliccinmu dukan abubuwan da ke damunmu ba sa’ad da muke addu’a, amma ya san abubuwan da muke yi da kuma dalilin da ya sa muke yin su. Ban da haka ma, idan yanayinmu ba ya barin mu mu yi wani abu mai kyau da muke so mu yi, Allah yana fahimtar hakan. Mafi muhimmanci ma, da yake Allah ya halicce mu a hanyar da za mu riƙa nuna ƙauna, yana jin daɗi idan ya gan mu muna nuna ƙauna.​—1 Yohanna 4:​7-10.

Nassosi sun tabbatar mana cewa

  • “Gama idanun Ubangiji suna a kan masu aikata adalci, kunnuwansa kuma suna jin kukansu.”​—1 BITRUS 3:12.

  • Yahweh ya ce, “Zan koya maka in kuma nuna maka hanyar da za ka bi. Zan ba ka shawara, ba zan cire idona a kanka ba.”​—ZABURA 32:8.

ALLAH MAI TAUSAYI NE SOSAI

Idan muka san cewa Allah yana fahimtar yanayinmu, shin hakan zai taimaka mana mu jimre matsaloli? Ka yi la’akari da abin da ya faru da wata mata a Najeriya mai suna Anna. Ta ce: “Saboda da yanayi mai wuya da nake fama da shi, na soma ganin cewa rayuwa ba ta da wani amfani. Ni gwauruwa ce kuma ina da ’ya da take fama da wata cuta a ƙwaƙwalwarta. Ban da haka, ina fama da ciwon kansar mama. Don haka, ana bukatar a yi mini tiyata don a cire kansar. Bai kasance mini da sauƙi in yi jinyar kaina da kuma ’yata a lokaci ɗaya ba.”

Me ya taimaka wa Anna ta jimre da wannan matsala? Ta ce: “Na yi tunani sosai a kan nassosi kamar Filibiyawa 4:​6, 7 da suka ce ‘Allah zai ba ku salama irin wadda ta wuce dukan ganewar ɗan Adam.’ A duk lokacin da na tuna da nassin nan, ina ƙara kusantar Jehobah don na san ya san ni sosai fiye da yadda na san kaina. Ƙari ga haka, ’yan’uwa a cikin ikilisiya sun taimaka mini sosai.”

“Har yanzu ina fama da rashin lafiyar, amma ni da ’yata muna samun sauƙi sosai. Tun da Jehobah yana tare da mu, ba ma yawan tunani marar kyau a duk lokacin da muka shiga matsala. Littafin Yaƙub 5:11 ya gaya mana cewa: ‘Ga shi, waɗanda suka jimre mukan ce da su masu albarka ne. Kun dai ji irin jimrewar da Ayuba ya yi, kun kuma san yadda Ubangiji ya albarkace shi a ƙarshe. Gama Ubangiji mai jinƙai ne, mai yawan tausayi kuma.’” Tun da Jehobah ya fahimci yanayin Ayuba, babu shakka yana fahimtar duk matsalolin da mu ma muke fama da su.

Hakika, Allah ya san kome. Ya san dukan matsalolinmu har ma da waɗanda mutane ba su sani ba ko kuma ba su gane da kyau ba