Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Allah Ya ba Dokokin Tsabta Gaba da Lokacinsu

Allah Ya ba Dokokin Tsabta Gaba da Lokacinsu

 Jim kadan kafin al’ummar Isra’ila ta shiga Kasar Alkawari wajen karnuka 35 da suka shige, Allah ya gaya musu cewa zai kāre su daga “mugayen cututtukan” da suka sani a Masar. (Maimaitawar Shari’a 7:15) Hanya daya da ya yi hakan ita ce ta wajen ba su umurnai game da yadda za su kasance da tsabta da kuma yadda za su hana cuta yaduwa. Alal misali:

  •   Dokar da aka ba al’ummar ta kunshi yin wanka da kuma wanki.​—Littafin Firistoci 15:​4-27.

  •   Allah ya gaya musu game da bayan gida cewa: “Za ku kebe wani wuri a bayan sansani inda za ku ta tafiya yin bayan gida. A cikin kayanku, sai ku sa abin tona kasa, domin sa’ad da kuka yi bayan gida a waje, sai ku tona rami ku rufe bayan gidan.”​—Maimaitawar Shari’a 23:​12, 13.

  •   Ana kebe mutanen da ake ganin sun kamu da cutar da za ta iya yaduwa na wani lokaci don kada cutar ta yadu. Kafin wadanda suka warke daga cutar su dawo sansanin wajibi ne su wanke tufafinsu kuma su yi wanka da ruwa kafin a dauke su a matsayin marasa “kazanta.”​—Littafin Firistoci 14:​8, 9.

  •   Duk wanda ya taba gawa za a kebe shi.​—Littafin Firistoci 5:​2, 3; Littafin Kidaya 19:16.

 Dokokin da aka ba Isra’ilawa game da tsabta sun yi daidai da shawarwarin masu kiwon lafiya a zamaninmu.

 A wasu wurare ba a bin wannan ka’idar ta tsabta. Alal misali:

  •   Ana zuba bayan gida a kan titi. Ana gurbata ruwa da abinci kuma ana zubar da shara da ke jawo cututtuka da kuma mutuwar yara.

  •   Likitoci a zamanin dā ba su san kome game da kwayoyin cuta ba. Masarawa suna amfani da abubuwa kamar su jinin kadangare da kashin tsuntsu da mataccen bera da fitsari da kuma burodin da ya bace don yin magani. Ƙari ga haka, suna amfani da kashin mutane da na dabbobin don yin magungunansu.

  •   TMasarawa a zamanin dā suna kamuwa da cututtuka da yawa saboda ruwan Nilu da aka gurbata da kuma ruwan da suke noma da shi. Ban da haka, yara da yawa suna mutuwa daga amai da gudawa da kuma wasu cututtuka sanadiyyar cin gurbataccen abincin.

 Amma Isra’ilawa sun amfana sosai daga bin ka’idodin Jehobah kuma sun kasance da koshin lafiya.