Koma ka ga abin da ke ciki

An Yi Wa Mutanen Sinti da Roma Wa’azi a Jamus

An Yi Wa Mutanen Sinti da Roma Wa’azi a Jamus

Mutanen Sinti da Roma masu dimbin yawa suna zama a kasar Jamus. * Kuma a kwana kwanan nan Shaidun Jehobah sun wallafa littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki da kasidu da kuma bidiyoyi a yaren da mutanen suke yi. *

A watan Satumba da Oktoba na shekara ta 2016, Shaidun Jehobah sun yi wani kamfen na musamman, kuma sun yi iya kokarinsu don su yi wa mutanen Sinti da kuma Roma wa’azi a yarensu. Sun yi hakan ne a birane dabam-dabam a kasar Jamus, har da birnin Berlin da Bremerhaven da Freiburg da Hamburg da kuma Heidelberg. Ban da haka ma, sun tsara yadda za su rika yin taro a yaren Romany a Majami’un Mulki da ke wurin.

Mutane Sun Saurara Sosai

Mutanen Sinti da Roma da yawa sun yi mamaki kuma sun yi farin ciki don wannan kamfen din. Wasu ma’aurata masu suna Andre da Esther da suke cikin wadanda suka yi wa’azin sun ce: “Mutanen sun yi farin ciki sosai don irin kokarin da muka yi don mu yi musu wa’azi.” Ban da haka ma, mutanen da suka ji sakon Littafi Mai Tsarki kuma suka karanta a yarensu sun yi murna sosai. Da aka nuna ma wata mata bidiyon nan Me Ya Sa Zai Dace Mu Yi Nazarin Littafi Mai Tsarki? a yaren Romany, matar ta yi ta kallon bidiyon kuma abin ya ba ta mamaki sosai har ta rika cewa, “Wannan yarenmu ne fa!”

Wani Mashaidi mai suna Matthias da yake cikin wadanda suka yi wa’azi a birni Hamburg ya ce: “Ni da matata muna cikin rukunin mutane takwas da suka je yin wa’azi a yankin da mutanen Sinti da Roma suke zama kuma mutanen da ke wurin sun kusa 400. Kuma duk wanda muka yi ma wa’azi yana son ya mu ba shi littafin da zai karanta.” Bettina wadda ta je yin wa’azi a birnin Hamburg ta kara da cewa: “Wasu suna zub da hawaye sa’ad da suka ga cewa Shaidun Jehobah sun wallafa littattafai a yaren Romany.” Kuma nan da nan da yawa suka soma karanta littattafan da babban murya, wasu har sun karbi littattafan da za su ba wa abokansu.

Mutanen Sinti da kuma Roma da yawa sun amince da gayyatar da aka yi musu na halartan taro. Kuma da yawa daga cikin mutane 94 da suka halarci taro a birnin Hamburg, ba su taba zuwa taron Shaidun Jehobah ba. A birnin Reilingen da ke kusa da garin Heidelberg, adadin mutane 123 ne suka halarci taro. Bayan haka, mutane biyar da suke yin yaren Romany sun ce a yi nazari da su.

A lokacin da aka yi kamfen din wa’azin, Shaidun Jehobah sun rarraba katsidu da warkoki kusan 3,000. Ban da haka ma, Shaidun sun yi wa mutanen Sinti da Roma fiye da 360 wa’azi kuma suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da guda 19. Da yawa daga cikin mutanen suka ce, “muna farin ciki cewa Allah yana son mu san shi.”

^ sakin layi na 2 Mutanen Sinti ba su da yawa kuma suna zama a Yammacin Turai ta tsakiya. Mutanen Roma ma ba su da yawa domin sun fito ne daga Gabashin Turai da kuma Kudu Maso Gabashin Turai.

^ sakin layi na 2 Kundin nan Encyclopædia Britannica Online ya ce mutanen Roma suna da “yaruka 60 ko kuma fiye da haka.” A wannan talifin, za a yi amfani da sunan nan “Romany” a matsayin dukan yaren da mutanen Sinti da kuma Roma da suke zama a Jamus suke yi.