Koma ka ga abin da ke ciki

Shaidun Jehobah Suna Tilasta wa Yaransu Su Bi Imaninsu Ne?

Shaidun Jehobah Suna Tilasta wa Yaransu Su Bi Imaninsu Ne?

 A’a, mutum ne zai tsai da shawarar bauta wa Jehobah. (Romawa 14:12) Shaidun Jehobah suna koya wa yaransu ka’idodin Littafi Mai Tsarki. Idan yaran suka yi girma, su za su tsai da wa kansu shawarar zama Shaidun Jehobah.​—⁠Romawa 12:2; Galatiyawa 6:⁠5.

 Kamar yawancin iyaye, Shaidun Jehobah suna so yaransu su ji dadin rayuwa. Suna koyar da yaransu abubuwan da suka san cewa zai amfani yaran, kamar aikin hannu da ka’idodi masu kyau da kuma addini. Shaidun Jehobah sun gaskata cewa bin ka’idodin Littafi Mai Tsarki zai sa mu ji dadin rayuwa. Saboda haka, suna yin iya kokarinsu don su koya wa yaransu ka’idodin Littafi Mai Tsarki ta wajen yin nazari da su da kuma halartan taro da su. (Maimaitawar Shari’a 6:​6, 7) Idan yaran sun girma, su za su tsai da shawara ko za su bi addinin iyayensa.

 Shaidun Jehobah suna yi wa jarirai baftisma ne?

 A’a. Littafi Mai Tsarki bai ce a yi wa jarirai baftisma ba. Alal misali, kafin Kiristoci a karni na farko su yi baftisma, sun saurari wa’azi kuma sun “yarda” da abin da suka ji. (Ayyukan Manzanni 2:​14, 22, 38, 41) Saboda haka, kafin mutum ya yi baftisma, ya kamata ya fahimci abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa, ya gaskata da abin da ya koya, kuma ya tsai da shawarar bin wadannan ka’idodin. Jarirai ba za su iya yin wadannan abubuwan ba.

 Sa’ad da yara suka yi girma, suna iya tsai da shawarar yin baftisma. Amma kafin su yi hakan, suna bukatar su san muhimmancin alkawarin da suke so su dauka.

 Shaidun Jehobah suna kin yaransu ne idan sun ki yin baftisma?

 A’a. Shaidun Jehobah ba sa farin ciki idan yaransu sun ki bin addininsu. Duk da haka, suna kaunar yaransu, ba sa kin yaran domin sun ki zama Shaidun Jehobah.

Ko da shekarun mutum nawa ne, shi ne zai tsai da shawara ko zai yi baftisma ko a’a

 Me ya sa Shaidun Jehobah suke fita wa’azi da yaransu?

 Akwai dalilai da yawa da ya sa muke fita wa’azi tare da yaranmu. a

  •   Littafi Mai Tsarki ya umurci iyaye su koya ma yaransu ka’idodin Allah. (Afisawa 6:⁠4) Da yake bauta wa Allah ta kunshi shaidar bangaskiya, yin wa’azi sashe ne mai muhimmanci na koya wa yara game da Allah.​—⁠Romawa 10:​9, 10; Ibraniyawa 13:⁠15.

  •   Littafi Mai Tsarki ya karfafa yara “su yabi sunan Ubangiji.” (Zabura 148:​12, 13, King James Version) Hanya mai muhimmanci da za mu yabi Allah ita ce ta koyar da mutane game da shi. b

  •   Yara sukan amfana idan sun fita wa’azi tare da iyayensu. Alal misali, sukan koyi tattaunawa da mutane dabam-dabam kuma suna koyan halaye masu kyau kamar tausayi da alheri da daraja mutane da kuma sadaukar da kai. Kuma hakan na taimaka musu su fahimci abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya ce game da imaninsu.

 Shaidun Jehobah suna yin bukukuwan hutu da kuma wasu bukukuwa ne?

 Shaidun Jehobah ba sa yin bukukuwan hutu ko kuma bukukuwan da ke bata wa Allah rai. c (2 Korintiyawa 6:​14-17; Afisawa 5:10) Alal misali, ba ma yin bikin tuna da ranar haihuwa ko bikin Kirsimati domin sun samo asali ne daga addinan karya.

 Ban da haka, Shaidun Jehobah suna jin dadin yin tarayya da iyalinsu da kuma ba yaransu kyauta. Suna yin tarayya da kuma ba da kyauta a kowane lokaci ba sai lokacin biki sau daya a shekara ba.

Iyaye Kiristoci suna jin dadin ba yaransu kyauta

a Yaran Shaidun Jehobah ba sa fita wa’azi ba tare da iyayensu ko kuma wasu da suka manyanta ba.

b Littafi Mai Tsarki ya ambata yara da yawa da suka faranta wa Allah rai ta hanyar koyar da wasu game da imaninsu.​—⁠2 Sarakuna 5:​1-3; Matiyu 21:​15, 16; Luka 2:​42, 46, 47.

d An canja wasu sunayen.