Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TATTAUNAWA TSAKANIN SHAIDUN JEHOBAH DA MUTANE

Me Ya Sa Ya Dace Ka Bincika Littafi Mai Tsarki?

Me Ya Sa Ya Dace Ka Bincika Littafi Mai Tsarki?

Tattaunawar da ke gaba misali ne na yadda Shaidun Jehobah suke yi wa mutane wa’azi. A ce wani Mashaidi mai suna Brian yana wa’azi kuma ya haɗu da wani mutum mai suna Eric.

LITTAFI MAI TSARKI YANA ƊAUKE DA TABBATACCEN TARIHI

Brian: Barka dai. Sunana Brian kuma na yi murnar ganinka. Naka sunan fa?

Eric: Sunana Eric. Amma gwamma na gaya maka tun da wuri, ni ba mai bin addini ba ne. Saboda haka, kada ka tsaya yin wani dogon bayani.

Brian: Na yi farin ciki da ka gaya min ra’ayinka. Amma bari in tambaye ka, ka yi girma a cikin iyalin masu bin addini ne?

Eric: E. Amma na fita sha’anin addini sa’ad da na bar gida don yin karatu a kwaleji.

Brian: Me ka karanta a makaranta?

Eric: Ilimin zaman al’umma da kuma tarihi. Tun asali ina son tarihi domin ina so in san yadda rayuwar ’yan Adam a duniya ta soma.

Brian: Hakika tarihi na da ban sha’awa. Shin ka san cewa Littafi Mai Tsarki ma littafin tarihi ne? Ka taɓa bincikensa kuwa?

Eric: A’a. Na san cewa Littafi Mai Tsarki littafi ne mai kyau amma ba na masa kallon littafin tarihi.

Brian: Yana da kyau kai ba mai tsattsauran ra’ayi ba ne. Idan kana da ɗan lokaci, zan so in nuna maka misalan tabbataccen tarihin da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

Eric: To, ba damuwa. Amma ba ni da Littafi Mai Tsarki.

Brian: Babu matsala. Zan nuna maka daga nawa littafin. Misali na farko yana cikin 1 Labarbaru sura 29, ayoyi 26 da 27. Ayoyin sun ce: “Hakanan ne mulkin Dauda ɗan Jesse bisa dukan Isra’ila. Shekararsa arba’in yana mulkin Isra’ila; shekara bakwai yana mulki cikin Hebron, shekara talatin da uku ya yi mulki cikin Urushalima.”

Eric: A wace hanya ce wannan ya zama misalin tabbataccen tarihi?

Brian: To dai, akwai lokacin da masu bincike suka ce Sarki Dauda bai taɓa wanzuwa ba.

Eric: Da gaske? Me ya sa ba su gaskata cewa ya wanzu ba?

Brian: Ban da shaida da ke cikin Littafi Mai Tsarki, babu isashen shaida da ta nuna cewa shi mutum ne da ya taɓa wanzuwa. Amma a shekara ta 1993, wasu masu tone-tonen ƙasa sun samo wani allon dutse ɗauke da rubutun da ke nufin “Gidan Dauda” da kuma “Sarkin Isra’ila.”

Eric: Bayanin na da ban sha’awa.

Brian: Wani kuma a cikin Littafi Mai Tsarki da aka yi shakkar wanzuwarsa shi ne wani gwamna da ya yi mulki a zamanin Yesu, wato Bilatus Ba-Bunti. An ambata shi a Luka sura 3, aya ta 1, tare da wasu jami’an gwamnati na zamanin. Don Allah, ga shi ka karanta.

Eric: To, ayar ta ce: “Bilatus Ba-Bunti yana mai-mulkin Yahudiya, Hirudus kuma yana muƙaddashin Galili.”

Brian: Na gode. A dā, wasu masana sun yi shakkar wanzuwar Bilatus Ba-Bunti. Amma wajen shekaru 50 da suka shige, an samo wani dutse a Gabas ta Tsakiya ɗauke da sunansa.

Eric: Hmm. Ban taɓa jin wannan bayanin ba.

Brian: Na yi farin ciki da na iya bayyana maka.

Eric: A gaskiya, na san cewa an tsara rubutun Littafi Mai Tsarki da kyau sosai, amma ban taɓa ɗauka cewa yana da wani muhimmanci a gare mu ba. Babu shakka, yana ɗauke da tabbataccen tarihi, amma a ganina ba shi da wani amfani a yau.

LITTAFI MAI TSARKI TSOHON LITTAFI NE MAI AMFANI YANZU

Brian: Mutane da yawa suna da wannan ra’ayin. Amma ra’ayina ya bambanta a kan wannan batun. Ga dalilin da ya sa na faɗa hakan: Tun da aka halicci ’yan Adam har zuwa yau, ainihin bukatunmu ba su canja ba. Alal misali, har wa yau muna bukatar abinci da sutura da kuma wurin kwance. Kowa zai so ya riƙa sadawa da mutane kuma iyalinsa su zauna lafiya. Ko ba haka ba?

Eric: Ƙwarai.

Brian: Littafi Mai Tsarki zai iya inganta rayuwarmu a dukan fannonin nan. Hakika, za mu iya ce da shi tsohon littafi da ke da amfani yanzu.

Eric: Waɗanne fannoni ke nan?

Brian: Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da ƙa’idodin da amfaninsu bai rage ba tun da aka rubuta su ƙarnuka da dama da suka wuce. Alal misali, idan ya zo ga batun kasancewa da ra’ayi da ya cancanta game da kuɗi ko iyali ko kuma zama abokin kirki, ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki za su iya yi mana ja-gora kuma su taimaka mana mu yi nasara a rayuwa. Za ka yarda cewa a zamaninmu, ba shi da sauƙi mutum ya zama miji da kuma shugaba mai kyau a cikin iyali, ko ba haka ba?

Eric: Haka ne. Ni da matata mun yi shekara ɗaya da aure amma da kyar ra’ayinmu ya zo ɗaya.

Brian: Gaskiya ne. Amma Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da ƙa’idodin da za su taimaka muku. Alal misali, ƙa’idodin da ke Afisawa sura 5, ayoyi 22 da 23 da 28. Don Allah, ga shi ka karanta mana wurin.

Eric: To. Wurin ya ce: “Mataye, ku yi zaman biyayya da maza naku, kamar ga Ubangiji. Gama miji kan mata yake, kamar yadda Kristi kuma kan ikilisiya ne, shi da kansa fa mai-ceton jiki ne.” Sa’an nan aya ta 28 ta ce: “Haka nan ya kamata mazaje kuma su yi ƙaunar matayensu kamar jikunansu. Wanda yake ƙaunar matatasa kansa yake ƙauna.”

Brian: Na gode. Shin ba gaskiya ba ne cewa idan mata da miji suka bi wannan shawarar, za su ji daɗin aurensu?

Eric: Gaskiya ne. Amma yin hakan ba cin tuwo ba ne.

Brian: A gaskiya, babu wanda ba ya kuskure. Saboda haka, kowace dangantaka tana bukatar sanin yakamata da kuma haƙuri. Littafi Mai Tsarki ya taimaka wa ni da matata mu san yadda za mu kasance da sanin yakamata.

Eric: Hakika wannan shawara ce mai kyau.

Brian: Shaidun Jehobah suna da dandali a Intane inda za ka sami shawarwari masu kyau a kan batun aure da kuma iyali. Idan kana da ɗan lokaci har ila, zan so in nuna maka misalin bayanai da za ka iya samu a dandalin.

Eric: Babu laifi.

Brian: Da kyau. Adireshin dandalin shi ne www.mt711.com/ha. Kalli shafin farkon.

Eric: Hotunan sun yi mini kyau.

Brian: Hotunan ’yan’uwanmu ne da ke wa’azi a faɗin duniya. Yawwa, ga sashen da nake so ka gani, wato sashen “Ma’aurata da Iyaye.” A wannan sashen, akwai tambayar da na san za ka so ka sami amsarta. Tambayar ita ce, “Me Zai Sa Iyalinka Ta Yi Farin Ciki?” Don Allah ka karanta mana jimloli biyu na ƙarshe a ƙarƙashin tambaya ta biyu.

Eric: To. Wurin ya ce: “Ya kamata mata da miji su nuna ƙauna da daraja ga juna. Tun da dukan maza da mata ajizai ne, gafarta wa juna yana da muhimmanci sosai domin yana kawo farin ciki a aure.” Hmm, ina son abin da aka faɗa a nan.

Brian: Sannu da karatu. Akwai nassin da aka rubuta a wurin, wato, Afisawa 5:33. Bari in buɗe maka don ka karanta.

Eric: Wurin ya ce: “Kowane ɗayanku shi yi ƙaunar matatasa kamar kansa; matan kuma ta ga kwarjinin mijinta.”

Brian: Idan ka lura, za ka ga an nanata cewa mata da miji su riƙa ba wa juna abin da ya dace da kowannensu.

Eric: Ban gane hausarka ba.

Brian: Abin da nake nufi shi ne, kowane namiji yana son matarsa ta girmama shi. Mace kuma tana so mijin ya nuna mata cewa yana son ta sosai.

Eric: Hakika, wannan gaskiya ne.

Brian: Idan a kowane lokaci mijin yana nuna wa matarsa cewa yana sonta, kana ganin matar ba za ta girmama shi sosai ba?

Eric: Kamar hakan zai taimaka.

Brian: To, ka gani cewa wannan nassin da aka rubuta kusan shekaru 2,000 da suka shige yana ɗauke da umurni mai kyau ga mata da miji kuma idan suka bi ta, za su amfana sosai.

Eric: A gaskiya, yanzu na gano cewa Littafi Mai Tsarki yana da muhimmanci fiye da yadda nake tsammani.

Brian: Na yi farin cikin jin hakan, Eric. Zan so in dawo don mu tattauna tambaya ta uku da ta ce, “Ya kamata ka rabu da matarka ne idan ba ka jin daɗin aurenku?” Wannan tambayar tana cikin wannan talifin har ila, a dandalinmu na Intane. *

Eric: To. Ni da matata za mu bincika shi tare.

Akwai wani batu a cikin Littafi Mai Tsarki da za ka so ka sami ƙarin bayani a kai? Za ka so ka sami ƙarin bayani a kan wasu daga cikin koyarwa ko kuma abubuwan da Shaidun Jehobah suka yi imani da su? Idan haka ne, ka sami Shaidun Jehobah don su yi maka bayani a kan waɗannan batutuwan. Za su yi farin cikin tattaunawa da kai

^ sakin layi na 56 Don ƙarin bayani, ka duba babi na 14 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da ƙa’idodin da amfaninsu bai rage ba tun da aka rubuta su ƙarnuka da dama da suka wuce