Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

Koyarwar Littafi Mai Tsarki Ta Gamsar da Ni

Koyarwar Littafi Mai Tsarki Ta Gamsar da Ni
  • SHEKARAR HAIHUWA: 1987

  • ƘASAR HAIHUWA: AZERBAIJAN

  • TARIHI: MAHAIFINTA MUSULMI NE, MAHAIFIYARTA KUMA BAYAHUDIYA

RAYUWATA A DĀ:

An haife ni a Baku, babban birnin Azerbaijan kuma ni ce auta a cikin ’ya’ya biyu da iyayenmu suka haifa. Mahaifina Musulmi ne, mahaifiyata kuma Bayahudiya. Iyayena suna son juna kuma addininsu bai shiga tsakaninsu ba. Mahaifiyata tana goyon bayan mahaifina a lokacin azumi na watan Ramadan, mahaifina kuma yana goyon bayanta a lokacin Idin Ƙetarewa. Muna da Alƙur’ani da Attaurat da kuma Littafi Mai Tsarki a gidanmu.

Na bi addinin mahaifina. Ban yi shakkar wanzuwar Allah ba amma na yi ta tunani a kan tambayoyin nan: ‘Me ya sa Allah ya halicci mutane kuma don me mutum zai sha wahala a duniya sa’an nan a sake azabtar da shi a jahannama?’ Ƙari ga haka, mutane suna cewa Allah ne yake ƙaddara kome, saboda haka na riƙa tunanin, ‘Shin Allah yana jawo wa mutane matsaloli sa’an nan ya yi musu dariya yayin da suke shan wahala?’

Na soma salla sau biyar a rana, sa’ad da na kai ’yar shekara 12. A lokacin, mahaifina ya tura ni da yayata wata makarantar Yahudawa, kuma an koya mana Ibrananci da al’adun Yahudawa da dai sauransu. Kafin a soma aji kowace rana, za mu yi addu’a bisa ga al’adar Yahudawa. Hakan ya sa ina salla a gida da safe, sa’an nan a makaranta, in yi addu’ar Yahudawa.

Na yi alla-alla in sami amsoshin tambayoyin nan. Sau da yawa na tambayi malamaina: “Me ya sa Allah ya halicci mutane? Yaya Allah yake ɗaukan mahaifina da yake shi Musulmi ne? Shi nagari ne, amma me ya sa ake masa kallon marar tsarki? Me ya sa Allah ya halicce shi?” Amsoshi ƙalilan da na samu ba su gamsar da ni ba.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA:

A shekara ta 2002, wani abu ya faru da ya sa na daina imani da Allah. Mun yi mako ɗaya ke nan da ƙaura zuwa ƙasar Jamus, sai mahaifina ya kamu da cutar shanyewar jiki har ya yi dogon suma. Zuwa lokacin, na yi shekaru ina roƙon Allah ya kāre iyalinmu kuma ya ba mu ƙoshin lafiya. Na roƙi Allah kowace rana kada babana ya mutu domin na yi imani cewa rai da mutuwa duk suna hannun Allah. A ganina ‘Allah ba zai yi banza da roƙon ƙaramar yarinya ba,’ saboda haka, na tabbata cewa zai amsa addu’ata. Amma sai mahaifina ya rasu.

Na yi baƙin ciki matuƙa domin a ganina Allah ya nuna mini halin ko-in-kula. Na soma tunani, ‘Ƙila ina addu’a ne a hanyar da ba ta dace ba ko dai Allah bai wanzu ba.’ Na rikice gaba ɗaya kuma na daina yin salla. Wasu addinan ma ban gane kansu ba, saboda haka na kammala cewa babu Allah.

Watanni shida bayan haka, Shaidun Jehobah suka ziyarce mu. Tun da yake ba mu ɗauki Kiristanci da muhimmanci ba, ni da ’yar’uwata mun so mu nuna musu cikin dabara cewa addininsu ba daidai ba. Muka tambaye su: “Me ya sa Kiristoci suke bauta wa Yesu da Maryamu da gicciye da dai sauran gumaka duk da cewa hakan ya saɓa wa Dokoki Goma?” Shaidun sun nuna mana a Littafi Mai Tsarki cewa bautar gumaka haram ne kuma ya kamata a yi addu’a ga Allah ne kaɗai. Hakan ya ba ni mamaki sosai.

Sai muka tambaye su: “Mene ne ra’ayinku game da koyarwar Allah-Uku-Cikin-Ɗaya? Idan Yesu ne Allah, ya aka yi ya zo duniya har mutane suka kashe shi?” Sai suka sake nuna mana cewa Yesu ba Allah ba ne kuma matsayinsu ba ɗaya ba ne. Shaidun suka ce domin wannan dalilin, ba su yi imani da koyarwar Allah-Uku-Cikin-Ɗaya ba. Amsoshinsu sun ba ni mamaki sosai kuma na ce wa kaina: ‘Lallai waɗannan wasu irin Kiristoci ne dabam.’

Duk da haka, na so in san dalilin da ya sa mutane suke mutuwa da kuma abin da ya sa Allah ya ƙyale mutane su sha wahala. Shaidun sun ba ni littafin nan Sanin Da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada, * kuma akwai wasu babi a ciki da ke ɗauke da amsoshin tambayoyina. Nan da nan suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ni.

A kowane nazarin da muka yi, na sami amsoshi a cikin Littafi Mai Tsarki da suka gamsar da ni. Na fahimci cewa sunan Allah Jehobah ne. (Zabura 83:18) Ba ya nuna son kai kuma yana ƙaunar kowa. (1 Yohanna 4:8) Ya halicci mutane domin yana so mu more rayuwa kamarsa. A hankali na fahimci cewa ko da yake Allah ya bar rashin imani ya kafu a duniya, ya tsani wannan halin kuma jim kaɗan, zai kawar da shi. Na kuma fahimci cewa rashin biyayyar Adamu da Hawwa’u ya jawo munanan sakamako ga ’yan Adam. (Romawa 5:12) Ɗaya daga cikin waɗannan sakamakon shi ne mutuwa, har da na mahaifina ma. Amma, a cikin sabuwar duniya da ke tafe, Allah zai kawar da matsalolin nan, kuma matattu za su sake rayuwa.—Ayyukan Manzanni 24:15.

Hakika, koyarwar Littafi Mai Tsarki ta gamsar da ni kuma na sake yin imani da Allah. Yayin da na ci gaba da yin tarayya da Shaidun Jehobah, na gano cewa suna ko’ina a duniya kuma suna nan kamar iyali guda. Haɗin kansu da kuma yadda suke ƙaunar juna ya ratsa zuciyata sosai. (Yohanna 13:34, 35) Abubuwan da na koya game da Jehobah sun sa ni sha’awar bauta masa. Saboda haka, na yanke shawarar zama Mashaidiyar Jehobah, kuma na yi baftisma a ranar 8 ga Janairu, 2005.

YADDA NA AMFANA:

Koyarwar Littafi Mai Tsarki ta sa na canja ra’ayina game da rayuwa. Sahihan amsoshin da na samu a cikin Kalmar Allah sun sa na sami kwanciyar rai. Na yi farin ciki sosai sa’ad da na koya cewa zan iya ganin mahaifina a nan gaba a lokacin tashin matattu kuma hakan ya ƙarfafa ni.—Yohanna 5:28, 29.

A yanzu haka, ni da maigidana Jonathan mun yi shekaru shida da aure, kuma shi mutumi ne mai tsoron Allah. Mun gano cewa koyarwar gaskiya game da Allah tana da sauƙin fahimta da kuma tamani. Shi ya sa muke farin cikin gaya wa mutane abubuwan da muka yi imani da su. Yanzu na san cewa Shaidun Jehobah ba “wasu irin Kiristoci” ba ne, amma Kiristoci ne na gaskiya.

^ sakin layi na 15 Shaidun Jehobah ne suka wallafa amma an daina bugawa.